5 Satumba 2021 - 09:21
Ayatullah Nuri Hamidani: Ayatullah Hakim Bai Taba Yin Kasa A Gwiwa Ba Wajen Neman Hakkokin Ba.

Dangane da rasuwar Ayatollah Hakim, Marji’in Shi’a ya jaddada cewa: “Baya ga rubutu da koyar da ilimomin Musulunci da yada al’adun Ahlulbaiti (AS) da horar da daliban ilimin addini, bai taba barin neman hakki ba. "

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) -Abna ya ruwaito, Ayatullah Nouri Hamedani ya aike da sakon ta'aziyyar rasuwar Ayatullah Sayyid Muhammad Sa’id Hakim.

Gundarin sakon da Marja’in shi'a ga shi kamar haka:

Da sunan Allah mai Rahama Mai Jinkai
Daga Allah muke kuma zuwa gare shi muke komawa
A ranar tunawa da shahadar Sayyidina Ali binul Husain, Zanul Abidin (A.S), rasuwar babban malami kuma Marji’I madaukaki mai girma Ayatullahi Haj Sayyid Muhammad Sa’id Hakim (Allah Ya yi masa rahama) wadan ya fato daga babban dangin na Ilami masana fikihu, jihadi da shahada, abu mai tsananin ciwo da damuwa.
Shi yakasance bayan koyar da koyarwar musulunci da yada al'adun Ahlulbaiti masu tsarki (A.S) da ilmantar da daliban ilimin addini, bai daina neman gaskiya ba. Jihadi don neman yardar Allah da jure zaman kurkuku na Hizbu Ba'ath tsawon shekaru da yawa ya bar tarihi abun koyi Mai Girma wajen tabbatar da gaskiya da rushe karya.
Ina mika ta'aziyya da tausayawa ga Sayyidina Waliyul Asr (Ruhin mu fansa a gareshi), Jagoran juyin juya halin Musulunci, manyan Maraj’ai ababen kwaikwayo, manyan makarantun Hauzozi na Najaf da Kum, dangin Rafi Hakim, musamman 'ya'yansa masoya, dalibai da masu qaunar Marigayi Sa’id.Kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wannan mamacin.

Hussain Nuri Hamidani